Shirin tattaunawa da tsagerun Niger-Delta | Labarai | DW | 07.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shirin tattaunawa da tsagerun Niger-Delta

Gwamnatin Najeriya ta bayyana aniyarta ta tattauna wa da mayagan na Niger- Delta masu aikata ta'asa kan bututan man fetir na kasar.

Karamin ministan harkokin man kasar ne dai Emmanuel Ibe Kachikwu ya sanar da wannan labari a ranar Litinin, kuma daman tuni rundunar sojojin na Najeriya ta aike da jiragen ruwa dauke da sojoji, da ma jiragen sama na yaki domin zakulo masu kokarin mayar da hannun agogo baya a harkokin hako danyan man na Tarayyar Najeriya.

Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya umarci sojojin kasar da su dakatar da shirin da suke yi domin bai wa masu tattauna wa damar samun warware wannan matsala ta hanyar ruwan sanyi.