Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
A cikin shirin za a ji yau ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin ilimi. Za kuma a ji yadda karatun 'ya'ya mata a jamhuriyar Nijar ke fuskantar kalubale.
Gwamnatin Najeriya ta bayyana damuwa a kan yaduwar kananan makamai a tsakanin jama'a ganin yadda hakan ya ke da illa musamman ga mata da kananan yara.
Harkokin yau da kullum na Nijar da ke makwabtaka da Najeriya na tafiyar hawainiya sakamakon zaben da ya gudana. A Maradi harkokin kasuwanci da zirga-zirgar jama'a sun sukurkuce saboda rufe kan iyakar kasashen biyu.
Sashen Hausa na DW na gabatar muku da wasannin kwallon kafa na lig-lig na Jamus wato Bundesliga kai tsaye ta rediyo.
9 ga watan Disambar ko-wace shekara rana ce da MDD ta ware domin tunatar da bukatar ci gaba da fafutukar kawar da cin hanci a tsakanin al'umma.