Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Shirin ya kunshi matakin gwamnatin jihar Legas na yaki da matsalolin muhalli. Akwai batun gazawar da gwamnatin Najeriya ta nuna a bangaren kudaden gudanar da al'amuran kasa. A Nijar kuwa wata Bajamushiya ce ta share wuri ta zauna a kasar.
Azumin watan Ramadan a bana ya zo cikin matsanancin hali na tattalin arziki a musanman a kasashen Afirka, abin da ya jefa Musulmi da dama cikin mawuyacin hali.
Shugaban Sashen Afirka na tashar DW Claus Stäcker na ganin rangadin aikin Olaf Scholz na farko a kasashen Senegal da Nijar da kuma Afirka ta Kudu na cike da nasara.
Gwamnatin Jamus karkashin jagorancin Angela Merkel ta mayar da hankali sosai a kan yammacin Afirka. Kama daga ayyukan raya kasa da batun bakin haure har zuwa batun tattalin arziki.
Za a iya cewa, babu wani yanki a duniya da Merkel ta mayar da hankali a kansa tsawon mulkinta kamar yammacin Afirka. Kama daga jibge sojojin Jamus a Mali da batun bakin haure har zuwa batun tattalin arziki.