Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
A cikin shirin za a ji cewa, wata tawaga ta kwararru ta yi nasarar kwance wani katafaren bam mai girma da aka dasa tun lokacin yakin duniya na biyu a birnin Cologne.
Bayan da Jamus ta dauki matakin mayar da wasu kayayyakin al'adu da aka sato lokacin mulkin mallaka, tawagar sarkin Bangwa daga Kamaru ta ziyarci Jamus din domin tattauna batun mayar da kayan.
Mahukunta a birnin Cologne na kasar Jamus sun amince da mayar wa Najeiya da wasu kayayakin tarihi da aka sace a masarautar Benin tun lokacin mulkin mallaka na Turawan Birtaniya.
Shugabannin kasashe bakwai masu arzikin masana'antu na duniya (G7) sun gana a kasar Japan.
Hatsaniya ya barke tsakanin jami'an 'yan sanda da masu fafutukar kare muhalli a kauyen Lützerath, a kan aikin hakar ma'adinai kwal don bunkasa makamashi a fadin Jamus.