Cikin shirin za a ji cewa a jihar Borno ta tarayyar Najeriya, an shiga mawuyacin hali a garin Rann Hedikwatar karamar hukumar Kala-Balge bayan da kungiyoyin agaji su ka dakatar da ayyukan jin kai saboda da harin da mayakan Boko Haram su ka kai inda suka hallaka wasu ma’aikatan jin kan tare da sace wasu.