1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabbin 'yan malisa na shirin fara aiki

May 2, 2023

Sabbin 'yan majalisar Najeriya na nazarin fara aiki cikin yanayin rashin kudi da dimbin bashin da ke barazana ga makomar kasar, dab da shirin mika mulki.

https://p.dw.com/p/4QoNR
Nigeria National Assembly
Zauren majalisar wakilan NajeriyaHoto: Nigeria Office of the House of Representatives

Taraiyar Najeriyar dai na fuskantar dimbin bashin da babu irinsa cikin kasar da ke biyan kaso 95 cikin 100 na kudaden shigar ta wajen biyan ruwa na bashin da ta ci.

Ko bayan rikicin rashin kudin da ke barazana ga makomar ta jihohin kasar da daman gaske ko bayan ita kanta Abujar da ke kallon raguwar kudin shigar man fetur.

To sai dai kuma sababbin 'yan mulki na kasar sun koma kuryar daki da nufin nazarin hanyar tunkarar rigingimun kudin da ma dabarun mulkin da ke shirin yin tasiri a kokarin cika alkawarin da ke tsakanin su da masu zabe na kasar.

Nationalversammlung in Abuja, Nigeria
Harabar majalisar wakilai ta AbujaHoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Wani taro na daukacin zababbun a Abuja dai na kallon hanyoyin kaiwa ya zuwa ilimantar da sabbabin mamallakan taraiyar Najeriyar da dabarun mulki na zamani da nufin iya kaiwa ga fita cikin rukukin bashin da ma cika burin sauya rayuwar al'umma

Ishaya Idi dai na zaman daya a cikin masu shirya taron na Abuja da kuma ya ce iya kaucewa ya zuwa hanci da ma sanin dabarun mulki na zamani na iya kaiwa ya zuwa jan aikin sauya makoma a cikin halin babun.

Cancanta ko kuma kokari na jari hujja dai, ko bayan annobar hancin dai, akwai kuma barazanar raba gari a tsakanin tsofaffi na jihohin da ke shirin barin gado da masu niyyar aikin.

Jihar kano dai alal ga misali na zama daya a cikin jihohin da ke fuskantar takaddama a tsakanin jam'iyyar APC da ke shirin barin gado da NNPP mai shirin hawa gado, kuma a fadar Comrade Aminu Abdusallam da ke zaman mataimakin zababben gwamnan jihar Kanon suna shirin dorawa ko ana ha maza ha mata a kokari na sauke hakki. 

Nigeria Politik l Senat
Zauren majalisar dottijan NajeriyaHoto: Getty Images/AFP/K. Sulaimon

Kokari na ceto ga Kano, ko kuma bakar siyasar gado, shekara da shekaru dai miliyoyi na 'yan kasa na fatan sauyi  na gwamnatin na iya kaiwa ya zuwa sauya makoma.

To sai dai kuma rikicin da ke a tsakanin bangarorin biyu dai a fadar Faruk BB Faruk da ke sharhi cikin batun na siyasa na nuna irin abun da ke shirin gani cikin kasar a nan gaba.

'Yan watannin da ke tafe dai na da muhimmancin gaske  cikin kasar da ke neman dorawa zuwa gaba amma kuma a cikin bakin duhu na siyasa mai wari.