Shin akwai hannun Kwankwaso a matsalar tsaro?
February 12, 2026
Duk da cewar dai an dade ana nunin yatsa bisa rawar siyasa cikin batun tsaron Najeriya, ambato sunan Rabiu Musa Kwankwaso a bangaren Amurka dai tuni ya tayar da hankali cikin gidan siyasa inda jagorar jar hula ke nuna alamun tashe.
Tasirin matakin
Har ya zuwa sabon shirin dokar ta Amurka dai, can cikin gidan tarihi babu bayanan da ke ta kokarin ta'allaka tsohon gwamnan na Kano ko dai da kokari na ta‘addanci balle batun na Kiristoci.
Kwankwason da ke zaman jagora a adawa dai na zaman na farkon fari cikin gidan na siyasa da sunansa ke fitowa fili a bakuna da kila ma a zuciyar ta Amurka cikin batun rashin tsraon mai tasiri.
Matsayin sauran 'yan siyasa
To sai dai kuma kama daga APC mai mulki ya zuwa ragowar jam'iyyun da ke cikin gidan na adawa dai ra‘ayi yana shiirn zuwa daya bisa rawar ta Kwankwaso cikin batun tsaron Najeriya. Adalci cikin batun tsaro, ko kuma neman dorawa kare laifin kura, ambato sunan na Kwankwaso na zuwa ne a yayin da fagen siyasar Najeriya yake dada daukar zafi.
A cikin neman kare kirista ne dai Amurkawan ke kokari na tsomin baki cikin fagen siyasar Najeriya. Kuma sabo na matakin yan dokar na Amurka dai a fadar Reverand Emmanuel Ozumba dake zaman daraktan ilimantarwa a kungiyar kiristocin Najeriya ta CAN bai zowa masu bin addinin na Kirista daban ba.
Ko ya zuwa ina Amurkawan ke fatan kaiwa a kokari na bankado masu rawa cikin batun na ta'adda, daga dukka na alamu shigar siyasa a cikin tsaron Najeriya, na iya sauya da dama cikin kasar nan gaba.
An dai ambato sunan na Kwankwaso a yayin da fagen siyasar Najeriya ke sauya launi da salo. 'Yan kwanaki da kila watannin da ke tafe na da tasirin gaske ga kokarin tantancewa a tsakanin bakar siyasar Najeriya da kokari na kare ta'adda.