Shekaru 65 da sanya hannu kan tsarin mulkin Jamus | Siyasa | DW | 23.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shekaru 65 da sanya hannu kan tsarin mulkin Jamus

Ra'ayin dukkan jam'iyyun siyasa a majalisar ya zo daya cewa tsarin mulkin na Jamus ya dace da wannan zamani wanda kuma ke da dokoki da za a iya yin koyi da su.

A wani biki da ta yi a ranar Jumma'a, majalisar dokokin Jamus ta Bundestag ta tuna da cika shekaru 65 da sanya hannu kan kundin tsarin mulkin Jamus, wanda aka yi a ranar 23 ga watan Mayun shekarar 1949. Ra'ayin dukkan jam'iyyun siyasa da ke da wakilci a majalisar ya zo daya cewa tsarin mulkin na Jamus ya dace da wannan zamani wanda kuma ke da dokoki da za a iya yin koyi da su.

A lokacin da yake jawabi a gun zaman bikin, shugaban majalisar dokoki ta Bundestag, Norbert Lammert ya ce kundin tsarin mulkin ya kasance abin murna a cikin tarihin Jamus da ma Jamusawa baki daya. A ranar 23 ga watan mayun 1949 wato yau shekaru 65 ke nan da aka amince da tsarin mulkin jim kadan bayan yakin duniya na biyu. Har yanzu kuwa shi ne ginshikin tsarin demokradiyar kasar, inji Nobert Lammert shugaba majalisar dokokin ta Jamus.

"Tun da jimawa tsarin mulkin na daga cikin manyan dokoki a duniya, yana zama wata alkibla ga sabbin tsare-tsare na demokradiya, yana zama abin sha'awa da ma koyi ga wasu kasashe."

Damar yin gyare-gyare don dacewa da zamani

Wani abu na musamman ga tsarin mulkin kamar yadda Lammert ya jaddada shi ne damar da ya bayar na yi masa gyaran fuska don ya dace da zamani, sannan ya ba da kariya ga 'yancin baki da sauran 'yan ci-rani da ke a kasar ta Jamus.

Berlin Joachim Gauck Einbürgerungsfeier im Schloss Bellevue 22.05.2014

Gauck da wata rike da shaidar zama Bajamushiya

Shi ma shugaban tarayyar Jamus Joachim Gauck a lokacin da yake mika wa wasu baki takardun shaidar zama Jamusawa a fadarsa da ke birnin Berlin yan jaddada kyawawan tanade-tanade da tsarin mulkin ya yi gami da muhimmancin da bakin ke da shi a ci gaban Jamus. Sannan da babbar murya ya yi kira da samun karin yawan baki da ke shigowa Jamus tare da yin kira ga Jamusawa da sum kara nuna hakuri ga sabbin 'yan kasar.

"Yanzu haka kasarmu ta fara gane gaskiyar cewa mutane na da dangankata da kasashe daban-daban amma duk da haka sun mayar da Jamus gida suna jin dadin rayuwarsu a cikinta. Kasar ta san cewa al'umma za ta kara zama abin sha'awa idan ta amince da wasu al'ummomin daban-daban. Ba tare da mayar wani saniyar ware ba."

Sai dai a lokaci daya Gauck ya tabo irin matsalolin da aka fuskanta da bakin, inda ya yi magana game da aikata laifi tsakanin matasa musamman baki da kirkiro da unguwannin marasa galihu da mayar tallafin da hukuma ke ba wa marasa karfi tamkar sana'a da rashin zuwa makaranta da ya fi yawa tsakanin yaran baki.

Matakan ba sani ba sabo ga masu aikata laifi

Ra'ayin Gauck ya saba da na shugabar gwamnati Angela Merkel wadda aka rawaito tana magana game da daukar matakan ba sani ba sabo a kan bakin musamman na kasashen tarayyar Turai da ke shigowa Jamus saboda karbar irin tallafin nan da gwamnati ke ba wa marasa aikin yi.

Bundestag Feierstunde Navid Kermani 23.05.2014

Navid Kermani

A bikin dai na wannan Jumm'a albarkacin cikar kundin tsarin mulkin Jamus shekaru 65 da samuwa, majalisar dokokin kasar ta gayyaci wani marubuci dan asalin kasar Iran, Navid Kermani dan shekaru 47 don yin jawabi. Bayan yabo da girmamawa da ya nuna wa tsarin mulkin kasar, Kermani ya yi suka ga canje-canjen da aka yi wasu sassan tsarin mulkin, inda ya ba da misali da 'yancin samun mafakar siyasa.

"Duk da cewa tsarin mulkin ya tanadi bude kofofin Jamus, amma kuma a wannan lokacin yana rufe kofofin kasar ga mutane da ke matukar bukatar taimakonmu saboda matsaloli na siyasa da gallazawa da suke fuskanta a kasashensu."

A karshe dai dan asali Iran din ya gode wa kasar ta Jamus dangane da damammakin da ta ba wa wasu 'yan kasar da ke da asali daga ketare.

Maswallafa: Richard Fuchs / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin