Sharhi kan ficewar Birtaniya daga EU | Siyasa | DW | 24.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sharhi kan ficewar Birtaniya daga EU

'Yan Birtaniya sun zabi matakin ficewa daga EU, sai dai duk da haka bai kamata EU din ta bar sakamakon maras dadi ya jefa ta cikin rudani ba inji Christoph Hasselbach na tashar DW.

Sakamakon wannan kuri'ar raba gardama wani bala'i ne ga kowa da kowa. Kuma kowa ya yi asara. Magoya bayan ficewar Birtaniya yanzu suna jin sun samu karin 'yancin kai, amma ba da jimawa ba za su gane ashe 'yanci ne na bogi. Kasar za ta kara talaucewa. Wani muhimmin abu ma shi ne Hadaddiyar daular Birtaniya ka iya rugujewa, domin mafi yawan al'ummar yankin Scotland sun zabi cigaba da zama cikin EU saboda haka za su iya neman ballewa daga Birtaniya. Kazalika kiraye-kirayen samun hadaddiyar kasar Ireland na kara yawa domin bayan ficewar Birtaniya yanzu iyakokin wajen na EU sun ratsa tsakiyar Ireland.

Ana tsammanin shiga wannan mummunan halin a sauran kasashen EU. Ba kawai rashin wata kasa mai ba da kaso mai tsoka a kasafin kudi ba, za a kuma yi rashin babban matsayi a manufofin ketare da diplomasiyya da karfin soji, domin Birtaniya ta taka rawa wajen ganin EU ta zama mai gogayya a duniya. Musamman Jamus za ta ji zafin rashin Birtaniya. Akwai wasu kasashen da ke son ganin EU din ta zama saniyar ware a duniya. Amma gwamnatocin Berlin da London sun zamo masu magana da yawu daya amma yanzu wannan kawa ta kau.

Christoph Hasselbach

Christoph Hasselbach na tashar DW

Wani tasiri da watakila ya fi muhimmanci shi ne na siyasa. Matakin na Birtaniya ka iya zama darasi da bai kamata a samu karin kasashe da za su su fice ba. Amma wasu kasashe za su iya bin sahu wajen yin barazanar kiran kuri'ar raba gardama, kuma kamar Birtaniya za su nemi karin iko na musamman. A karshe wata EU za ta rage wadda kowace memba za ta nemi samun abinda ya fiye mata amma ba tare da daukar wani nauyi ba.

Da yawa daga cikin kasashen Eu na son Birtaniya ta dandani kudarta bayan wannan mataki. Za kuma su nuna halin ba sani ba sabo domin ya zama darasi ga wadanda za su so yin koyi da ita. Sai dai hakan ba zai yi kyau ba. Duk mai ramuwar gayya ya san cewa hakan zai kara wa makiyyan EU farin jini ne. Duk wata barazana a nan za ta kara dagula halin da ake ciki ne. Abinda ake so yanzu shi ne natsuwa sannan a yi kokarin kulla sabuwar dangantaka da 'yan Birtaniya. Shakka babu wannan ba za ta maye gurbin zama memba a EU ba, amma matakin ba sani ba sabo ba zai haifar da abin kirki ba.

Dole ita kanta EU ta yi karatun ta natsu a kan manufofinta, domin ba komai ne hedkwatar kungiyar a birnin Brussels za ta iya magance wa ba. Ga misali matsalar 'yan gudun hijira da ya zame wa nahiyar wani kalubale mafi girma. Dole a gaba a inganta hadin kai tsakanin kasashen Turai kan matakan magance daidaikun matsaloli. Lokaci ya wuce da EU za ta yi ta danganta kanta da wani aikin neman zaman lafiya, amma ta na watsi da wasu muhimman batutuwa. Matakin da Birtaniya ta dauka tamkar wani mugun mafarki ne da lokacin guda ke zama kira na yin zurfin nazari da yin karatun ta natsu kan abubuwan da a tare za a iya cimmawa a nan gaba.

Sauti da bidiyo akan labarin