1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana jimamin mutuwar kocin kwallon kafa

Ramatu Garba Baba
September 15, 2019

Shahararren mai horas da 'yan wasan kwallon kafar Rudi Gutendorf, ya rasu yana da shekaru 93 bayan da ya kai kololuwa tare da kafa tarihi a dabarun murza leda.

https://p.dw.com/p/3Pcui
Rudi Gutendorf
Hoto: picture-alliance/dpa/F. P. Tschauner

Gutendorf dai ya yi fice a ciki da wajen kasar Jamus, an san shi da hazaka da jajircewa kan duk wani abu na wasan tamola, aikin horas da 'yan wasa ya sa shi karade duk nahiyoyin duniya, inda ya gudanar da aikin horas da 'yan wasa na kungiyoyi fiye da hamsin a kasashen duniya sama da talatin.

Dan marigayin Fabian ne ya sanar da mutuwar gwarzon kocin a daren jiya Asabar, rashin da ma'abota kwallon kafa ke ci gaba da nuna alhininsu a ciki dama wajen kasar ta Jamus. Rudolf 'Rudi' Gutendorf dai ya rasu ne a sakamakon tsufa kamar yadda babban dan nasa ya fadi.