Sankarau na ci gaba da kisa a Najeriya da Nijar | Siyasa | DW | 12.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sankarau na ci gaba da kisa a Najeriya da Nijar

Kungiyar likitoci masu bayar da agaji ta duniya ''Doctors Without Borders'' ta fitar da rahoton cewar cutar Sankarau da ta kashe akalla mutane 836 a Najeriya, ita ce mafi muni da aka samu tun farkon shekara ta 2016.

A cewar rahoton kungiyar ta Medicine Sans Frontairs a turancin faransa, akalla mutane 10,000 ne suka kamu da cutar ta sankarau rukunin C wadda kuma ita ce mafi hatsari a Najeriya a wannan shekara kadai.

Rahoton ya ce jihohin Sokoto da Zamfara da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya ne cutar ta fi kamari cikinsu a kwanakin baya, inda masu kamuwa da ita kan rasa karfin garkuwar jiki, da raunin kwakwalwa da kuma na laka.

Hukumomi a tarayyar ta Najeriya dai na bayyana nasarar kakkabe cutar baki daya, amma ga alama akwai sauran rina a kaba. A wata ziyara da DW ta kai kauyen Bagarawa na karamar hukumar Bodinga a jihar Sokoto, mutanen kauyen sun ce har yanzu cutar na nan cikin jama'a.

Rahoton na Medicine Sans Fronteirs, haka nan ya bayyana shakku a kan karancin magungunan sabuwar cutar da aka yiwa lakabi da type C a dai dai lokacin da cutar ke ci gaba da kashe mutane. Ko a kwanakin nan ma inji mazauna kauyen Bagarawa an rasa rayuka a sakamakon wannan cuta.

Sai dai a ta bakin kwamishinan lafiya na jihar Sokoto Dr. Balarabe Shehu Kakale, sankarau ta zama tarihi a jihar Sokoto idan aka yi la'akari da kwararan matakan da gwamnati ta dauka.

Cutar ta sankarau dai cuta ce mai saurin yaduwa da kisan jama'a cikin hanzari.

Sauti da bidiyo akan labarin