1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sanatoci sun yi watsi da bukatun Tinubu a Nijar

August 5, 2023

A wani abun da ke zaman gagarumin koma baya ga tunanin amfani da karfi wajen sake mai da mulkin Nijar, majalisar dattawan Najeriya ta yi fatali da bukatar shugaba Bola Tinubu.

https://p.dw.com/p/4UoiA
Nigeria Abuja | ECOWAS Gipfel
Hoto: Kola Sulaimon/AFP/Getty Images

A wani abun da ke dada nuna alamun barazana ta fito na fito tsakanin kasashen yankin da ke barazanar afkawa Nijar da sojan da ke dada nuna alamun ko mutuwa ko yin rai. To sai dai kuma daga dukkan alamu miliyoyin al'ummar Nijar din sun yi nasarar tsira daga fuskantar  rikicin soja tare da majalisar dattawan Najeriyar fatali da bukata ta shugaban kasar ta afkawa Nijar din in ta kama.

Cikin wani zama na musamman da yammaciyar yau din nan ra'ayi ya zo iri guda a zauren majalisar na kaucewa hatsin a matsayin hanyar tilasawa masu juyin mulkin komawa ga bariki. Kundin tsarin mulkin taraiyar Najeriyar dai ya haramta duk wani kokari na kai yaki wajen kasar ba tare da sahalewar dattawan yan dokar tarrayar najeriyar ba.

Tun daga farkon fari dai dabara ta hatsin tana da burin aiken sako ga zuciyar sojin yankin da ke kara nuna alamun kwadayin mulki bayan alkawarin kallo daga nesa a lokaci mai nisa akwai dai tsoron tsaiwa irin ta gwamin jakin sojan Nijar din na iya zama kafa ta kara tsomin bakin soja a kari na kasashen ECOWAS dake dada fuskantar matsalolin tsaro da tattali na arziki.

A  wannan Lahadi (6.08.2023) ne dai wa'adin kungiyar kasashen ECOWAS ke shirin karewa bisa bukatar komawar sojan Nijar zuwa a bariki.