Sakin ′yan matan Chibok 21: Nasara ga gwamnatin Najeriya | Siyasa | DW | 13.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sakin 'yan matan Chibok 21: Nasara ga gwamnatin Najeriya

An nuna farin ciki a Abuja sakamakon gano wasu jerin 'yan matan makarantar Chibok da aka sace sama da shekaru biyu.

Tun cikin watan Afrilun shekara ta 2014 ne dai wani samamen 'yan kungiyar ta Boko Haram ya yi sanadiyyar sace yaran 276 daga wata makarantar kauye da ke garin Chibok na jihar Bornon Najeriya.

Duk da cewar dai an yi nasarar gano daya a cikin 'yan matan a farko na shekarar nan dai, nasarar ta sakin 'yan matan dai ta sanya jami'ai na gwamnatin kasar kasa tsaye.

Mr Femi Adesina dai na zaman kakakin fadar gwamnatin kasar ta Aso Rock, kuma a fadarsa ranar na zaman ta farin ciki da ma annashuwa ga gwamnatin.

"Lallai gwamnati tana farin ciki saboda batu ne da ke tsakiya ta zuciya ta jami'ai na gwamnatin, saboda haka rana ce ta farin cikin da ba shi misaltuwa a garemu musamman ma ganin fara samun nasarar da aka yi a yau. Muna kuma da fata mai yawan gaske na samo ragowar 'yan matan."

Tuni dai aka kawo 'yan matan zuwa Abuja sannan kuma aka hada su da likitoci da nufin duba lafiyarsu kafin daga baya a mika su ga mataimakin shugaban kasar a hedikwatar hukumar tsaron cikin gidan DSS da ta yi uwa makarbiyar ceto su.

Duk da cewar Abujar ta kai ga musanta musaya, amma majiyoyin tsaron cikin gidan DSS din dai sun ce akalla kwamandoji na kungiyar guda hudu ne dai aka mika wa kungiyar a wani abun da ke zaman alamu na gini na aminci a tsakanin juna, kafin kaiwa ga sakin 'yan matan da kusan dukkaninsu suka kuma zama iyaye tare da 'ya'yansu.

Sabuwar barazana ta rikicin darikun Shi'a da Sunni

To sai dai kuma in har Tarrayar Najeriyar ta yi nasarar kulla aminci da kila ma kai karshen Boko ta Haramun, wata sabuwar barazanar da ke nuna alamun kunno kai na zaman rikici na darika a tsakanin mabiya darikar Shi'a da na Sunni a kasar.

Nigeria Schiitische Muslime in Dakasoye (A. Abubakar/AFP/Getty Images)

Zanga-zangar 'yan Shi'a a Najeriya

Akalla mutane 13 ne dai aka tabbatar da hallakasu a wani rikicin da aka gwabza a jihohin Kaduna da Katsina da Kano da Sakkwato a sashen arewacin kasar.

Barazanar kuma da a cewar Dr Jibo Ibrahim da ya taka rawa wajen binciken rikicin 'yan Shi'ar da sojoji a Zaria ke iya kaiwa ga jefa kasar a cikin sabon rikicin addini.

Kurkuku na daure da dama ko kuma rikici na addini a tsakanin 'yan uwa da abokai, har ya zuwa ranar yau dai babu martani na gwamnatin game da kisan da ke zaman irinsa mafi muni tun bayan fito na fiton na Zaria.

Kokari ta ji daga baki na gwamnatin dai ya kare tare da kakakin na Abuja na fadin ranar na zaman ta farin ciki maimakon tuna bacin ran na ranar Laraba a fadar Femi Adesinan.

"A'a, a'a muna murnar ceto 'yan matan nan ne abun da kawai za mu iya magana kai ke nan yanzu."

A na sa ran bayan kamalla ganawarsa da 'yan matan dai jami'ai na fadar gwamnatin kasar a karkashin mataimakin shugaban kasar za su  yi wa manema labarai jawabin abun da idanuwansu suka kalle musu can.

Sauti da bidiyo akan labarin