Bude sabon babin huldar tsakanin EU da AU
January 10, 2020Talla
Shirin wanda zai hada a wuri daya batun yaki da yinwa da kuma talauciya, da huldar kasuwanci da batun 'yan gudun hijira da yaki da gurbatar muhalli, tanadi cimma yarjejeniya tsakanin kungiyar ta EU da kuma takwararta ta AU a karkashin jagorancin kasar Jamus.
Tuni dai majalisar dokokin Turai ta sanya hannu kan kudirin dokar kafar sabuwar huldar wacce amma za ta bayar da muhimmanci ga batun mutunta hakkin dan Adam wajen aiwatar da ita.