Sabuwar alaka tsakanin Buhari da Saraki | Siyasa | DW | 02.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sabuwar alaka tsakanin Buhari da Saraki

A Najeriya an kama hanyar samun kyautatuwar dangantaka tsakanin shugaban kasar Muhmmadu Buhari da shugaban majalisar dattawan kasar Bukola Saraki.

Hoton da ya janyo mai da martani a Najeriya

Hoton da ya janyo mai da martani a Najeriya

A karon farko cikin watanni uku tun bayan da aka zabe shi a matsayin shugaban majalisar dattawan Najeriya an ga shugaban majalisar na raha har da dariya shi da shugaban kasar Muhammadu Buhari, yanayin da a wattani ukun da ya yi yana jagorantar majalisar bayan hasashen zaman tankiya a tsakanin bangarorin biyu ba a taba gani ba.

Rikicin Shugabanci

Rikicin majalisar dokokin Najeriya

Rikicin majalisar dokokin Najeriya

Yadda Sanata Bukola Saraki ya dare kan mulkin shugabancin majalisar ya haifar da zaman tankiya a tsakanin majalisar dattawan da ma samar da bangarori biyu na Unity Forum da Like minds, inda ta kai ga kama hanyar baiwa hammata iska a tsakanin bangarorin biyu, kana zaben na Saraki bai yi wa jam'iyyarsa ta APC dadi ba. Wannan sauyi dai na zama alamar da ka iya samar da mafita a kasar.

Sanin cewa a lokutan baya dai an ruwaito cewa shugaban majalisar dattawan Najeriyar ya yi iyakar kokarin ganawa da shugaban Najeriya ba tare da samun nasara hakan ba, a yanzu da aka ga wannan sauyi ko wane tasiri zai yi ga yanayin gudanar da majalisar? Alhaji Isa Tafida Mafindi gogaggen dan siyasa ne a Najeriyar ya ce hakan na da matukar muhimmanci ga dorewar siyasar kasar.

Faretin ranar 'yancin kai a Najeriya

Faretin ranar 'yancin kai a Najeriya

Zaman tankiya a majalisun Najeriya

A majlisun dokokin da suka gabata dai zaman tankiya a tsakanin bangarori biyu na zartaswa da na majalisar dokokin Tarayyar Najeriyar ya kawo cikas ga gudanar da gwamnati musamman fanin yi wa talakawa aiki, abin da ya sanya nuna damuwa a kan halin da majalisar ta takwas ke ciki a yanzu, musamman a gwamnati APC da ita ce ta farko ta ‘yan adawa da ta kai ga madafan iko a kasar. Abin jira a ganin dai shi ne ko za'a ga canji da ma dorewar dangantakar a tsakanin sassan biyu, musamman sanin cewa shugaban majalisar dattawan na fuskantar shari'a a kotun da'ar ma'aikata bisa zargin kin bayyana kadarar da ya mallaka?

Sauti da bidiyo akan labarin