Sabbin matakai na kawar da kungiyar IS | Labarai | DW | 27.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabbin matakai na kawar da kungiyar IS

Iraki ta amince ta hada kai da Rasha da Siriya wajen musayar bayanai na sirri a yakin da aka daura da 'yan kungiyar nan ta IS da ke rajin girka daular Islama.

Mai magana da yawun Firaministan Iraki din haidar al-Abadi wato Saad al-Hadithi ya ce kasashen sun amice da girka wani kwamiti da zai maida hankali wajen musayar bayanai na sirri kuma tuni Iraki ta bada wanda zai wakilce ta.

Kwamitin inji al-Hadithi zai kuma sanya idanu ne kan irin motsin da dakarun IS din ke yi daga waje zuwa waje da kuma yin kokari na dakile irin karfin da suke da shi.

Gabannin wannan dai, Rasha ta aike da jiragen yakinta da dakaru Siriya kana shugaban Rasha din Vladmir Putin zai tattauna da wasu takwarorinsa musamman ma Barack Obama nan gaba kadan kan wannan batu.