Yayin da wa'adin babban bankin tarrayar Najeriya kan tsoffin takardun Naira ke karatowa, rudani da rashin tabbas sun mamaye daukacin kasar saboda rashin samun sabbin takardun kudin
Dubban kanana da matsakaitan 'yan kasuwa a Najeriyar na cikin tsaka mai wahalar gaske sakamakon gaza canjin kudaden a yayin da wa'adin karshe na watan Janairun ke kara karatowa.
Kama daga babban birnin tarraya Abuja ya zuwa jihohin kasar da daman gaske tuni 'yan kasuwa suka fara kin karbar tsoffin kudaden yayin da kuma sabbabin babu su a gari.
Abin jira a gani dai na zaman yadda take shirin kayawa a tsakanin babban bankin dake neman sauyin zamani, da kuma sauran jama'ar garin dake fadin ana gaggawa.