1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Najeriya ta takaita fitar da kudade a bankuna

Ubale Musa ZUD/SB
December 7, 2022

Babban Bankin Najeriya, CBN, ya ce daga ranar tara ga watan Janairu na 2023 an takaita yawan kudin da kowanne dan kasar zai iya cirewa daga asusun bankinsa zuwa Naira 100,000 a mako guda.

https://p.dw.com/p/4KbV0
Hoto: Ubale Musa/DW

Gwamnatin Najeriya dai  ta fara wannan yunkurin da sake fasalin tarkardun wasu kudaden kasara makonnin baya, kafin fito da wannan sabon tsarin na rage yawan takardun kudin a hannun 'yan kasar. A kullum an takaita wa kowanne dan kasar cire kudin da ba su wuce naira 20,000 ba, a yayin kuma da a duk mako ba a yarda wani ya haura naira dubu 100 a hada-hadar ta takarda ba. An dai takaita su kansu kamfanoni a kasar da ta'amalli da takardar da bata wuce naira 500,000 a mako ba.

Burin tsarin dai shi ne rage tasiri na takardu na kudi cikin hada-hada ta tattali na arzikin al'ummar Tarrayar Najeriyar. Sabon tsarin da ke shirin sauya da dama ga rayuwa da ci-gaban al'umma dai na daukar hankalin miliyoyi na 'yan kasar da ke da babban sabo a cikin harkoki na takarda na kudi.

Kama daga annobar kudaden fansa ya zuwa uwa-uba batun cin hanci dai CBN na neman sauya da dama a cikin sabon tsarin da ke zaman ba sabunba. Dr Hamisu Yau dai, kwwarrare kan tattali a Abuja, ya ce ana shirin ji a jiki kafin iya kai wa ga fahimtar tsarin da kila samar da moriyarsa tsakanin al'umma.

''Tsarin zai rage hada-hada a tsakanin mutanen Najeriya da ba sa amfani da banki'' in ji Dr. Yau

Asusun bayra da lumuni na duniya, IMF, ya ce sama da mutane miliyan saba'in ne ke rayuwa aNajeriya ba tare da asusun ajiya a bankunan kasar ba. Batun tsaro dai na zaman na kan gaba cikin sababbin manufofin CBN da suka kasa kaiwa ga shawo kan amfani da kudade da nufin aikata laifuka cikin kasar. Dubban miliyoyin nairori ne 'yan bindiga ke karba a hannun mutanen da aka yi garkuwa da su a kasar.

''Idan ba dauki matakan hana ma'aikatan bankunan Najeriya karya irin wannan dokar fitar da kudin a asirce ba, to da kamar wuya idan dokar za ta yi tasiri.''  Dr. Kabir Adamu, mai sharhi kan harkokin tsaro ya shaida wa DW.

Waso masana a cikin kasar kuma na ganin sabon tsarin zai yi tasiri musamman a yayin zaben Najeriya da ke tafe. Masu irin wannan ra'ayin na cewa zai yi wuya idan har masu sayen kuri'a za su iya yin nasara ta amfani da bankuna.