1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Tsugune ba ta kare ba bayan sauya launin Naira

December 21, 2022

Mako guda da kaddamar da sabon kudin da aka sauya masa fasali a Najeriya har yanzu sabon kudin bai kai ga shiga hannun jama'a da dama inda ake zargin jabun sabon kudin ya cika kasuwanni.

https://p.dw.com/p/4LHwd
Sabon kudin Najeriya na Naira
Sabon Kudin NajeriyaHoto: Ubale Musa/DW

Zumudi da ‘yan Najeriya ke yi na samun sabbin takardun kudin da aka sabunta a kasar ya fara zama tsoro da fargaba saboda tsawon mako guda da fara fidda kudin a hukumance ba su wadatu a hannun mutane ba. Mutane da ke zuwa bankuna domin karbar kudin sun bayyana cewa tsofin takardun kudin ake ba su maimakon sabbin da suke dokin samu inda bankunan ke bayyana mu su cewa ba su da isassun sabbin takardun kudin shi ya sa ake ba da tsaffin.

Karin Bayani: An kaddamar da sabbin takardun Naira

Sabon kudin Najeriya na Naira
Sabon Kudin NajeriyaHoto: Ubale Musa/DW

Da yawa al'umma musamman ‘Yan kasuwa na dari darin karbar sabbin takardun kudin saboda fargabar karbar jabun kudaden wanda su ka fara tawa tsakanin al'umma. Masana harkokin kudi da tattalin arzikin kasa kamar Malam Shehu Abubakar na bayyana yadda wannan yanayi zai shafi harkokin kasuwanci da tattalin arzikin kasa.

Kokarin da na yi domin ji daga bankunan da ke ba da kudin ya ci tura domin kuwa dukn jami'an da na tuntuba sun ki yin magana a kai. Yanzu haka dai babban Bankin Najeriya fitar alamu na yadda za a gane takardun kudin da abubuwan da suka banbanta su da jabun kudin a wani bangare na ilmantar da mutane yadda za su kaucewa fadawa tarkon masu buga takardun kudin na jabu.