1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Najeriya: Wa'adin sake fasalin Naira

Uwais Abubakar Idris
October 27, 2022

Sanarwar da babban bankin Najeriya CBN ya bayar ta sauya fasalin takardar kudin kasar ta Naira a kokarin daidaita tasirinta, daidai lokacin da tattalin arzikin kasar ke cikin mawuyacin hali ta janyo mayar da martani.

https://p.dw.com/p/4Ilid
Najeriya | Naira | Tattalin Arziki | Fasali
Da ma dai darajar kudin Najeriyar wato Naira, ta jima da faduwa kasa wanwarHoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Babu dai zato ba tsammani babban bankin Najeriyar ya sanar da aniyarsa ta sake fasalin takardar kudin Nairar, tare kuma da bayar da wa'adi na lokacin da za a kaddamar da sababbin kudin zuwa ranar 15 ga watan Disambar wannan shekara. Wannan dai ya nuna sun kammala duk wani aiki a kan wannan aniya tasu, abin da zai shafi takardun kudi na Naira 100 da 200 da 500 da kuma 1000. Gwamnan babban bankin Najeriyar Godwin Emefiele ya ce canza takardar kudin ta Naira zai taimakawa manufara nan ta rage amfani da kudi a hannu, sannan ya taimaka maido da kudin cikin babban bankin ta fanin hada-hada. Ya kara da cewa sun yi amanna, matakin zai sa a samu raguwar ayyukan ta'addanci da garkuwa da mutane domin bukatar kudin fansa.

Najeriya | 'Yan Bindiga | Mutane | Kudin Fansa | Sata
Baya ga Boko Haram, 'yan bindiga na sace mutane domin neman kudin fansa a NajeriyaHoto: DW/Katrin Gänsler

Ana kallon matakin a matsayin dabara ta kokarin maido da kudin da suke a hannun jama'a zuwa bankin Najeriyar, tun da zai zama tilas ga kowa ya yi kokarin kai kudinsa banki. Babban bankin Najeriyar CBN dai ya bayar da wa'adin kwanaki 47 ga al'ummar Najeriyar, su mayar da tsofaffin kudin da za a canza. A baya dai irin wannan canji na kudi ya haifar da matsaloli, hakan ta sanya Dakta Isa Abdullahi Jos kwararre a fanin tattalin arziki ya ce akwai bukatara mayar da hankali wajen dawo da darajar Naira maimakon wannan mataki. Amma ga Malam Yusha'u Aliyu ya ce, akwai bukatar nazarin amfanin da ke tattare da wannan a halin da Najeriyar ke ciki. Tuni dai aka fara tururuwa zuwa bankuna domin shigar da wadannan takardun kudin Naira da za a canza, inda aka ga karuwar bukatar takardun kudin kasashen waje musamman dalar Amirka da Euro.