1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rudanin siyasar Rivers: Ina makomar Wike?

Muhammad Bello ZMA
January 6, 2026

Rikicin siyasar jahar Rivers na dada kazanta bisa ga jan layin da bangarori biyu masu rikici da juna suka yi.

https://p.dw.com/p/56Q7j
Ezenwo Nyesom Wike
Hoto: Getty Images/AFP/Y. Chiba

Masu sha'awa a rikicin kama daga matakin siyasar jahar ta Rivers da ma ta tarayya ke ci gaba da daukar bangare, wadda kuma hakan, masana harkokin siyasa na fassara shi da rigimar neman matsayi a zabukan shekarar 2027.

Rikici na siyasar jahar ta Rivers dai a yanzu, da tun farko ke ta'allaka kan tsarin siyasa wato Political Structure, da ke musamman matakin kananan hukumomin jaharwadda ke zamowa tinkahon ko wane dan siyasa, inda kuma a yanzu ta bayyana rigimar da ke tsakanin bangarorin gwamnan jahar Sim Fubara da kuma na tsohon gwamna Nyesom Wike yanzu ta ta'allaka ne kan batun wa ke da ta cewa a gurbin takarar kejerar gwamnan jahar a zabukan shekarar 2027 da ke tunkarowa.

Wata 'yar jarida mai sharhi Oby Ndukwe ke nan ke cewar da zarar mutum ya samu wani matsayi, to zaa fara ganin karakainar Yan bani na iya da ke bada shawarar yadda zaa yi, da kuma ke da manufa irin ta su.

Nigeria Fubara Rivers Ausnahmezustand
Hoto: Muhammad Bello

Rikicin siyasar dai da ya somo tun shekarar 2023, aza dokar ta baci a jahar, da kuma sulhu bayan dokar ta baci, ba su sa ya lafa ba. Nyesom Wike dai na ci gaba da dagewar cewar akwai yarjejeniyar cimma maslaha da ta hada da cewar ba gwamna Sim Fubara, ba sake takarar 2027 kuma Wike din ya yi barazanar sawa a buga wannan yarjejeniyar a jarida don duniya ta gani. Shi kuwa gwamna Fubara tuni bayan sauya sheka zuwa jamiyyar APC ya yi fatali da yarjejeniyar da Wiken ke magana, inda ya nunar ba mai hana shi takara. Hakan dai na kara fusata magoya bayan Wike din da ma Wike din kan sa.

Shugaban majalisar jahar ta Rivers Rt Hon Martns Amaewhule da ke goyon bayan Nyesom Wikeke nan ke cewar, wani Furucin baya bayannan na Gwamna Fubara ya kara fusatamu, kuma shine dalilin ganawa da 'yan jarida don bayyana ainihin halin da ake ciki, na cewar, Nyesom Wike mai kaunar jahar Rivers ne,da son zaman lafiya da son ci gaban jahar mu.

Gwamna Sim Fubara dai, da wasu ke ganin ya dade ya na kwanton kawowa wannan gaba, ya dada bayyana jan layin da ke tsakanin su da bangaren Nyesom Wike, tare ma da ci gaba da tantance wadan basa tare da su a wannan tafiya a wani taron magoya bayan sa. Sim Fubara ya ce haduwar mu a nan zai kara bamu damar sanin wadan da ke tare da mu.

Tuni dai shugaban jam'iyyar APC na jaha da ma kasa, da kumama da daman Gwamnonin jahohin da jamiyyar ta APC ke mulki kimanin 30, ke nuna mubayi'ar su ga Gwamna Sim Fubara na sake tsayawa takara, batun kuma da Nyesom Wike ke cewar mataki ne na binne shi da siyasar sa dungurungun, da kuma sai inda karfin sa ya kare.

Nigeria Abuja 2025 | APC National Executive Committee Meeting
Hoto: Ubale Musa/DW

Nyesom Wike ke nan ke cewar, ba tun yanzu muka fara wannan yaki ba a matakin kasa da ma na jaha, babu wani da zai zo don an bashi dama ya fimu kafafa, duk da cewar wasu daga cikin mu sun yi gaban kan su a siyasance, kuma wadanda suka bi mu ba za mu bar s,u su wahala ba a rayuwa.

Rikicin dai na Rivers yanzu da Nyesom Wike ke zargin gaggan 'yan siyasar jahar ke rura shi, ya fara shafar batun kasafin kudin jahar na supplementary da aka bukata a baya, da kuma na sabuwar shekara ta 2026 da mu ke ciki, dubi da cewar yawancin 'yan majalisun da za su sahale kasafin kudin, masu mubayi'a ne ga Nyesom Wike da ke adawa da gwamnan.

Nyesom Wike din dai yanzu, tuni ya dau matakin yin rangadin daukacin kananan hukumomin jahar 23, da wasu ke ganin salo ne na sake hade kan jama'arsa da ke neman dare masa watakil.