1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Najeriya: Rikicin siyasar jihar Rivers ya dagule

Muhammad Bello SB
December 5, 2025

A Najeriya 'yan majalisa 16, ciki har da shugaban majalisar na jihar Rivers sun sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyya mai mulki ta APC. Ragowar 'yan majalisu uku da suke mubayi'a ga gwamna, ba su ce uffan ba.

https://p.dw.com/p/54rL6
Gwamna Siminalayi Fubara na Jihar Rivers da ke Najeriya
Gwamna Siminalayi Fubara na Jihar Rivers da ke NajeriyaHoto: Muhammad Bello

Akwai alamu na rikicin bangarori biyu na siyasar jihar Rivers ya sake kunno kai, dubi da yadda shugaban majalisar jahar ya gabatar da wasu jawabai mai suka ga bangaren zartarwa bisa jagorancin Gwmamna Siminalayi Fubara, da kuma batun matakin 'yan majalisa 16,ciki har da shugaban majalisar, na sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyya mai mulki ta APC mai mulki a kasat. Ragowar 'yan majalisu uku da suke mubayi'a ga Gwamnan jahar Fubara, ba su ce uffan ba tukunna.

Alamomin rikicin

Gidan gwamnatin jihar Rivers da ke Najeriya
Gidan gwamnatin jihar Rivers da ke NajeriyaHoto: Muhammad Bello

Alamun wannan sabon rashin jituwa dai tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara na jihar ta Rivers, da kuma bangaren majalisar jihar ya fara bayyana ne bayan shugaban majalisar jihar Hon Martns Amaewhule ya fitar da wasu bayanai masu kakkausan suka ga bangaren majalisar zartarwa karkashin shugabancin Gwamna Fubara, kan cewar an rasa yadda kudade kimanin Naira biliyan 600, da Kantoman rikon jihar yayin dokar ta baci, Rear Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas mai ritaya, ya bari a asusun gwamnati.

Shugaban majalisar ya koka kan yadda kusan komai ya tsaya cak a jihar tun bayan dawowarsu kan karagar mulki yau watanni biyu ke nan.

Shugaban majalisar dai, yayin wani zama da sauran 'yan majalisar jihar 16 kawai, ya koka kan yadda bangaren zartarwa ba ya yin abin da ya kamata a fannin gudanar da ayyuka a jihar.

Sauya shekar 'yan majalisar dokokin

Ibok-Ete Ekwe Ibas tsohon Kantoman jihar Rivers tare da Shuaba Bola Tinubu na Najeriya
Ibok-Ete Ekwe Ibas tsohon Kantoman jihar Rivers tare da Shuaba Bola Tinubu na NajeriyaHoto: Ubale Musa

Ana tsaka da wannan gurmin ne kuma, majalisar jihar ta Rivers, karkashin jagorancin Martns Amaewhule, ta sanar da matakin sauya shekar 'yan majalisa 16 daga cikin 19, na ficewa daga jam'iyyarsu ta PDP zuwa jami'yya mai mulki ta APC, sakamakon dalilin cewar wai rikice-rikice sun ki ci-sun ki cinyewa a PDP.

To sai dai sauran 'yan majalisa uku da tun asali mubayi'arsu ga Gwamna Fubara take, ba su ayyana ficewa ba, kuma ma bayanai sun tabbatar, tun dawowa kan mulki bayan dage dokar ta baci, kafarsu ba ta taka majalisar ba ko da sau daya

Haka kuma shi ma kansa Gwamna Siminalayi Fubara da tun ba yanzu ba ake ta rade-radin zai sauya shekarsa zuwa APC, bai ce uffan ba tukuna. Hakan dai na ci gaba da yin wata manuniya ga yadda siyasar jihar take neman komawa, wato na zaman doya da manja, mai cike da sabon rikici.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani