1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kawo karshen rikicin siyasa a Rivers?

Muhammad Bello LMJ
September 18, 2025

Gwamnan Rivers da ke Najeriya Sim Fubara ya sake karbar ragamar mulkin jihar, bayan dakatar da shi tsawon watanni shida da aka yi karkashin dokar ta-baci da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kafa a jihar.

https://p.dw.com/p/50i73
Najeriya | Rivers | Gwamna | Sim Fubara
Gwamnan jihar Rivers a Najeriya Sim FubaraHoto: Muhammad Bello

Al'umma daga kananan hukumomin jihar ta Rivers da ke Najeriya 23 ne suka yi tururuwa, domin tarbar gwamnan nasu Sim Fubara. Tuni dai 'yan majalisar dokokin jihar da suma dokar ta-baci da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kafa ta shafa, suka koma bakin aiki.

Bankwana da kantoma

Ibok Ete Ibas da aka nada a matsayin kantoma, ya bar jihar tun ranar Laraba da daddare, bayan ya yi wa al'umma bayanin cewar ya cimma nasarar dukkan dalilan da suka sa aka kawo shi. Shagulgulan dakon dawowar gwamnan dai tun safiyar Alhamis, bayan ayyana dawowar gwamnan da mataimakiyarsa Mrs Ngozi Odu bakin aiki.

Tattaunawa da AIG Usaini Muhammad Gumel

A yayin zaman da suka yi bayan sun dawo bakin aiki, 'yan majalisar dokokin jihar ta Rivers sun bukaci gudanar da bincike kan shugabancin Kantoma Ibok Ete Ibas na watanni shida da kuma bukatar gwamna ya mika musu sunayen kwamishinonin da zai nada kana sun kuma sa hannu kan dokar kashe kudin gwamnati, karkashin jagorancin Martns Amaehwule.

Ko Gwamna Fubara na da kalubale a gabansa?

Dawowar Gwamna Sim Fubara kan kujerarsa ta gwamna wani abu ne kana azamar da zai sa a yanzu a matsayinsa na gwamna mai cikakken iko shi ma wani abu ne, lamarin da yanzu ke jan hankulan masu ruwa da tsaki a jihar ta Rivers. Kawo yanzu dai akwai 'yan gunaguni da ke fitowa kan yadda tsarin sababbin nade-naden da zai yi a gwamnatinsa za su kasance.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani