Rikicin Kirimiya na Ukraine na daukan sabon salo | Labarai | DW | 07.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Kirimiya na Ukraine na daukan sabon salo

Kasashen Turai da Amirka sun soki matakin kuri'a kan ballewar Kirimiya daga Ukraine tare da hadewa da tarayyar Rasha.

Kungiyar Tarayyar Turai da kasar Amirka sun yi tir da matakin da majalisar Kirimiya ta dauka na gudanar da zaben raba gardama bisa yuwuwar hadewa da Rasha. Yayin taron mambobin kungiyar da ya gudana a birnin Brussels na kasar Belgium, kasashen na Turai sun ce akwai mummunan sakamako da Rasha za ta fuskanta muddin ba a warware rikicin ba. Kasar Jamus ta shiga sahun masu neman magance matsalar ta hanyar diplomasiya. A wannan Alhamis da ta gabata shugaban Amirka Barack Obama ya yi hira ta wayar tarho kan lamarin da shugaban Rasha Vladimir Putin.

A daya hannun kasar Amirka ta dauki kakaba takunkumi na tattalin arziki da tafiye-tafiye kan wasu da ke adawa da gwamnatin Yukren.

Rasha ta tura dakaru bayan faduwar gwamnatin Viktor Yanukovich, wanda yake goyon bayan kasar ta Rasha. Tuni firaministan gwamnatin wucin gadi na Yukren Arseniy Yatsenuk ya ce babu wanda zai amince da zaben na raba gardama kan ballewar Kirimiya daga Yukren, domin hadewa da Rasha.

Mawallafi: Suleiman babayo
Edita: Mohmmad Nasiru Awal