Rashin tabbas kan tsaron Afghanistan | Labarai | DW | 14.04.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rashin tabbas kan tsaron Afghanistan

Amirka ta shawo kan sauran kasashen da ke cikin rundunar kawance a shirinta na son janye sojojinsu daga kasar Afghanistan bayan kwashe sama da shekaru ashirin.

Jamus ta bi sahun Amirka a shirin janye dakarunta daga kasar Afghanistan kamar yadda aka tsara za a yi a watan Satumbar wannan shekarar da muke ciki, wannan na zuwa ne jim kadan da sanarwar da Shugaban Amirka Joe Biden yayi, na kwashe sojojin kasar da suka kwashi fiye da shekaru ashirin suna yakar mayakan Taliban.

Baya ga Jamus ma, Britanniya da sauran kasashen mambobi na kungiyar tsaro ta NATO, sun baiyana anniyarsu ta janye sojojin. Amirka ta nemi hadin kan kawancen da suka mara mata baya a shiga yakin Afghanistan, da su mata biyayya a ficewa daga kasar a lokaci guda. Matakin son janye rundunar, na daga cikin dabarun da ake ganin, ka iya bai wa kasar ta Afghanistan damar tafiyar da lamurran tsaronta ba tare da taimakon wata kasa ba. Masana na ganin matakin na tattare da hadura na bar wa mayakan Taliban da suka hana zaman lafiya damar cin karensu ba babbaka.