Rasha ta yi tir da takunkuman EU a kan Kirimiya | Labarai | DW | 18.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha ta yi tir da takunkuman EU a kan Kirimiya

Rasha ta ce sabbin takunkumin da Kungiyar Tarayyar Turan ta kakaba wa yankin tsibirin Kirimiya ba abin karbuwa ba ne.

Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta ce sabbin takunkuman Kungiyar Tarayyar Turai, da suka haramta zuba jari a yankin Kirimiya ba abin karbuwa ba ne ko kadan, kuma wariya ne aka nuna wa yankin na tsibirin tekun Bahar Aswad wanda Mosko ta mayar karkashinta a cikin wata Maris. A cikin wata sanarwa ma'aikatar ta ce kamata ya yi EU mai shalkwata a birnin Brussels ta san cewa ba za a iya raba yankunan Kirimiya da Sebastopol da Rasha ba.

A wannan Alhamis Kungiyar Tarayyar Turai ta sanya takunkumin hana zuba jari a yankin Krimiya, musamman a fannonin samar da makamashi da mai da iskar gas da kuma harkokin sufuri da na sadarwa. Sannan za a hana jiragen ruwan Tarayyar Turai bi ta tekun Bahar Aswad. A ranar Asabar sabbin takunkuman za su fara aiki.