Rasha ta tallafa wa NIjar da takin zamani
February 24, 2026
Wannan tallafi ya zo a lokacin da ake bukatarsa a cewar babbar kungiyar manoman shinkafa ta kasa FUCOFRI kasancewar takin ya yi tsada sosai a kasuwa hasali ma kuma ba a samun mai kyau a kasuwannin. Shugaban kungiyar manoman shinkafar Bachirou Saga, ya yi kiran cewa idan har kasa ta samu irin wannan taki babban abun da ya kamata shi ne bada shi ga manoman na gaskiya.
Daga nashi bangare shugaban kungiyar manoma da makyaya ta kasa ta plate forme paysanne Djibo Bangna, ya nanata cewa duk kasa mai son ci gaba sai ta magance matsalar abinci ta hanyar bunkasa harkokin noma da kiwo.
A kasar Nijar yan kasuwa na dukufa aikin noma a wani mataki na bunkasa harkokinsu na kasuwanci da kuma burin samar da abinci ga kasa a cewar Honorable Alhaji Mou'azou Tchangalla, tsohon dan majalisar dokoki kuma manomi.
Kasar Nijar dai ta rungumi sabuwar tafiya, inda hukumomin suka dage da ganin kasar ta samu cikaken 'yanci a a kowane fanni musamman fannin abinci.
Tuni dai ofishin ministan kula da harkoki noma na kasar Nijar ya tabbatar da cewa takin na daf da isa kasar Nijar. shima a nashi bangare jakadan Rasha a Nijar ya tabbatar da hakan, lamarin da ke nuni da karfin huldar da ke tsakanin kasashen biyu.