1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha na barazana ga Amirka kan makamai

Yusuf Bala Nayaya
February 20, 2019

Putin ya ce duk wani yunkuri na Amirka na ajiye sabbin makaman nukiliya a wata kasa ta Turai wannan na nufin Rasha ba ta da zabi face ta mayar da martani.

https://p.dw.com/p/3DkgL
Russland | Putin hält Rede zur Lage der Nation | 2019
Hoto: Getty Images/AFP/A. Nemenov

Kasar Rasha ta bayyana cewa za ta mayar da martani ga Amirka duk lokacin da ta kuskura ta kai makamai masu linzami masu cin gajeran zango da ma matsakaicin zango. Shugaba Vladimir Putin ya bayyana haka a wannan Laraba. Da yake jawabi ga 'yan majalisar dokokin kasar ta Rasha Putin ya ce martanin Rasha ba zai tsaya ga kasashen da aka girke makaman ba kawai har da ita kanta kasar ta Amirka.

Putin ya ce duk wani yunkuri na Amirka na ajiye sabbin makaman nukiliya a wata kasa ta Turai wannan na nufin Rasha ba ta da zabi face ta mayar da martani saboda barazana da take fuskanta. Ya ce Rasha shirye take ta yi abota da Amirka amma kuma da shiri na kare kanta kuma.