Ranar Tunawa da juyin mulki na farko a Najeriya
January 15, 2013Daukacin alumman jihohin arewacin Najeriya da sauran kungiyoyin dake fafatukar ci-gaban mazauna yankunan suka yi wani binkin nuna juyayi da tunawa da ranar da aka yi wa marigayi Sardaunan Sakoto Ahmadu Bello da Alhaji Abubakar Tafawa Balewa da sauran gaggan 'yan siyasar yankin dangane da irin kisan gillar da aka yi masu.
Kowace ranar 15 ga watan Janairu, ranace ta musanman ga rayukan daukacin jama'ar jihohin arewacin 19, musanman kan kisan gillar da aka yi wa tsaffin shugabannin jamhuriya ta farko Sir Ahmadu Bello da Alhaji Abubakar Tafawa Balewa, bisa la'akari da irin gagarumar gudunmawar da suka bada wajan gina kasar batare da nuna wani banbancin kabilanci ba ko na siyasa, ballan ta na ma na addinai.
A shekarun ba ya dai gidan Sardauna wanda aka sani da Arewa House na kasancewa makil da mutane daga ko'ina a Najeriya da ma wasu kasashen Afrika makwabta dan ganin bajakolin kayayyakin da aka kashe Sardauna da su da kuma bude cikin gidan don masu ziriyara su yi kallon tarihi, inda masana tarihi da suka wallafa takardu a kan Sardaunan Sokoto ke bayayyanawa masu zuwa ziyara gidan cikakkun bayanai. Bikin dai ya zo dai dai da ranar tunawa da sojojin Najeriya da suka mutu a kan aikin kare kasar.
Mawallafi: Ibrahima Yakubu
Edita: Usman Shehu Usman