1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Olaf Scholz ya isa a Ukraine

Abdourahamane Hassane
February 14, 2022

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya isa a birnin Kiev na Ukraine inda yake tattaunawa da Shugaba Volodymyr Zelensky kan barazanar da Rasha take yi na mamaye Urkaine.

https://p.dw.com/p/4704z
Besuch Olaf Scholz Ukraine Wolodymyr Selenskij
Hoto: Press/ Presidential Office Ukraine

Zelensky da Scholz na tattauna samar da hanyoyin warware takun sakar da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine, kafin daga bisani  ya isa a birnin Moscow inda zai tattauna da Shugaba Vladmir Putin. Kungiyar kasashe masu karfin arzikin masantu G7 ta yi gargadin cewar nan ba da dadewa ba, za ta kakaba wa Rasha takunkumin karya tattalin arziki idan har ta kuskura ta mamaye Ukraine.