Nijar: Yara 12,000 ne ba sa zuwa makaranta a Diffa | Labarai | DW | 06.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nijar: Yara 12,000 ne ba sa zuwa makaranta a Diffa

Mafi akasarin makarantun yaran sun kasance a rufe a yankunan da ke kusa da tafkin Chadi da gefen kogin Yobe, a iyakokin kasashen biyu.

Oberschüler in Tahoua, Niger

'Yan makaranta a yankin Tahoua

Kimanin yara 'yan makaranta 12,000 ne ba sa samun damar zuwa makaranta a yankin Diffa da ke a Kudu maso Gabashin jamhuriyar Nijar a cewar Majalisar Dinkin Duniya a ranar Juma'an nan.

Mafi akasarin makarantun yaran sun kasance a rufe a yankunan da ke kusa da tafkin Chadi da gefen kogin Yobe da ke zama kan iyaka tsakanin Najeriyar da Nijar a cewar ofishin da ke lura da harkokin jama'a na Majalisar Dinkin Duniyar.

Ofishin ya ce makarantu 151 ne aka rufe wadanda ke da yara 'yan makaranta sama da 12,000 wadanda suka watse tare da malamansu bayan shiga dimuwa a lokutan hare-haren mayakan Boko Haram.