1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Rashin tallafin ketare ke sanya mu bunkasa hakar mai

December 6, 2022

Hukumomin Nijar sun ce rashin samun tallafi daga manyan kasashen duniya ne ke sanya su neman arziki ta hanyar mai.

https://p.dw.com/p/4KZ9w
Hoto: Presse- und Kommunikationsdienst der Präsidentschaft von Niger

Ministan kudi na Jamhuriyar Nijar Ahmat Jidoud ya ce rashin samun tallafi daga kasashe masu arziki na duniya ne ke kara tilasta wa kasar ci gaba da shirinta na bunkasa hakar man fetur duk da fargabar lalata muhalli da ake tsammanin shirin zai haifar wa kasar. 

A shekara ta 2011 ne dai Nijar ta shiga cikin jerin kasashen da ke hako danyan mai a yankin Damagaram a karkashin wata yarjejeniya da ta kulla da gwamnatin China. Kuma a watan Yuli na shekara mai zuwa kasar ke sa ran fara sayar da fetur dinta a kasuwar duniya. Ministan ya jaddada cewa idan har ba su samu kudin shiga daga mai da suke hakowa ba, to kokarin kasar na kyautata rayuwar jama'a ka iya dusashewa.