Nijar: Rufe wuraran kahar zinariya na Liptako | Labarai | DW | 18.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nijar: Rufe wuraran kahar zinariya na Liptako

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun sanar da rufe wuraran tonon zinariya na yankin Liptako da ke kudu maso yammacin kasar, inda dubban mutane 'yan kasar ta Nijar da na kasashen waje ke tonon zinariyar.

Tödliche Kinderarbeit in Nigeria Minen (DW/A. Kriesch)

Yara masu neman karfen Zinare

Akalla dai mutane 20.000 'yan kasar ta Nijar da sauran 'yan kasashe irin su Burkina Faso, Mali, da ma 'yan kasar Senegal ne ke ayyukan hakar zinariyar, inda wasu daga cikinsu ke wannan aiki tsawon shekaru 30 da suka gabata a cewar wata majiya ta yankin na Liptako.

 Wata sanarwa ce dai da ofishin ministan ma'adinan kasar ta Nijar ya fitar a wannan Talatan ta sanar da wannan mataki. Sai dai kuma sanarwar ba ta kayyade dalillan rufe wurare ba, amma kuma wani jami'in ofishin ministan ma'adinan kasar ta Nijar da bai so a bayyana sunan shi ba, ya ce gwamnatin ta dauki matakin ne domin kawo karshen rishin tsarin da ke wakana wajen tonon zinariyan da zimmar kawo sabin tsare-tsare na zamani a nan gaba ta yadda gwamnati za ta ci gajiyar lamarin.