Nijar ta yi asarar sojoji mafi girma a Inates
December 19, 2019Talla
Wannan shi ne irinsa hari na farko mafi muni da rundunar sojojin Nijar din ta fuskanta a cikin sama da shekaru goma, wanda ta rasa sojoji 71 a sakamakon hare-haren da kungiyar IS ta kai a sansanin sojojin Inates da ke a yammacin kasar kan iyaka da mali. Yanzu haka wannan hari ya janyo muhawara a sahun al'umma da ke zargin sojojin Faransa da mara wa 'yan ta'addar baya.