1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Jana'izar sojojin da suka mutu a fagen daga

Salissou Boukari AMA
December 13, 2019

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun ware zaman makoki na kawanki uku domin nuna alhinin ga sojojin kasar da suka mutu a wani harin ta’addanci a Inates mai iyaka da kasar Mali.

https://p.dw.com/p/3Ul4t
Niger Armee | Opfer nach Angriff
Hoto: DW/S. Boukari

Harin da ‘yan ta’adda na yankin arewacin Mali suka kai a barakin sojan Nijar na Inates na ci gaba da daukar hankullan jama’ar kasar inda jikin kowa ya yi sanyi tare da nuna juyayi da kuma fushi kan yadda lamari na ta’addanci ya samu gindin zama a wasu yankuna na kasar dabam dabam ta Nijar. Shugaban kasa Issoufou Mahamadou ya karrama jerin sunayen sojojin da suka rasa rayukansu, inda ya kuma jinjinawa sojojin kan irin bajintar da suka nuna ba tare da sun ja da baya ba wajen bai wa kasa da ‘yan kasa kariya ina ya ce "Gamu a yau mun hadu mu duka a mun sa gawawakin mutanten da ke da babban maihhamnci a garou mu duka. Mun hadu ne cikin bakin cikin rashinsu da mukayi ta hanya ta rashin imani da aka nuna musu. Da dama daga cikinsu sun mutu cikin yarintarsu wajen bamu kariya." A karshe Shugaban Issoufou Mahamadou ya daukaka sojojin ta hanyar kara musu girma duk da cewa basu raye tare da bai wa sojoji hudu da suka hada da baban komandan barakin na Itanes da ya yi tsayin daka na cewa ba zai ja da baya ba. Wannan makokin na faruwa ne a yayin da daidai lokaci guda kuma an samu yawaitar kashe kashen masu garuruwa a yankunan da ke iyaka da kasar da Mali da ma Burkina Faso. Wannan yanayi da kasar ta tsinci kanta na ci gaba da saka ayoyin tambaya a zukatan al’umma, inda a kullu yaumin jama'a ke neman sanin ta ina ‘yan ta’addan ke samu makamman da suke kai wadannan hare-hare, kuma suna da masaniyar dukannin wasu mahimman wurare da ke cikin barakin sojojin da suka kai wa hari.