Kasashen yankin Sahel na tataunawa | Labarai | DW | 15.12.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasashen yankin Sahel na tataunawa

Shugabannin kasashen yankin Sahel na G5 na gudanar da taron a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar domin kara neman hadin kai tsakanin kasashen don yaki da ta'addanci.

Shugabannin na tattauna halin da kasashen yankin na Sahel suka samu kansu na hare-haren da suke fuskanta daga kungiyoyin 'yan ta'adda. Wannan taro  na musammun na zuwa ne  bayan hare-haren da IS ta kai a barakin soji na Inates da ke kan iyaka da Mali wanda a ciki sojojin Nijar 71 suka rasa rayukansu. Daman dai shugabannin na kungiyar G5 sun shirya yin taron na Yammai gabannin halarta gayatar da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya yi musu a Pau domin tattauna batun tSaro a yankin wanda daga bisani aka dage saboda harin Inates.