Neman agajin duniya a kan Ebola | Labarai | DW | 10.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Neman agajin duniya a kan Ebola

Shugabannin kasashen da ke fama da annobar Ebola a yankin yammacin Afirka sun nemi da a basu agajin gaggawa domin shawo kan cutar da ke neman zama wutar daji.

Shugaban kasar Saliyo Ernest Bai Koroma da ta Laberiya Ellen Johnson Sirleaf ne suka yi wannan kira yayin da suka halarci taron Bankin Duniya ta hanyar tattaunawa ta wayar tarho. Taron wanda aka gudanar da shi a birnin Washington na Amirka ya samu halartar sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon wanda kuma ya kara jaddada bukatar aiki tare domin kare lafiyar dukkan al'umma. Bala'in annobar cutar ta Ebola dai kawo yanzu ya hallaka mutane sama da 3,400 a yankin yammacin Afirka yayin da wani dan asalin kasar Laberiya ya kasance mutum na farko da ya mutu a Amirka.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu