Laberiya na cikin kasashen yankin yamamcin Afirka kuma kalmar tana nufin masu 'yanci. Ta samu 'yanci tun 1847 lokacin da aka kai bayi bakaken fata daga Amirka.
Ta kasance jamhuriya mafi dadewa a Afirka, sannan bisa tabarbarewar harkokin siyasa da rayuwa kasar ta fusaknci kazamin yakin basasan cikin shekarun 1990 da ya kai ga mutuwar mutane masu yawa.