1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Zaben share fage na jam'iyyar APC

September 28, 2018

Bayan share tsawon lokaci da kuma sauya ranar zabe, jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta fara shirin fidda gwani na shugaban kasa da sauran manya na mukamai na siyasa.

https://p.dw.com/p/35frH
Abuja, Partei Kongress der in Nigeria regierenden APC
Hoto: DW/U.Musa

 

Sau uku dai ake saka rana tare da sake dagawa a bangare na jam'iyyar APC mai mulki da ke fatan bin 'yar tinki wajen kafa tarihi na zabe na dan takara ta shugaban kasar. Duk da cewar dai jam'iyyar tana da dan takara daya tilo da ke da bukatar tsaya mata takara na shugabanci a zaben na wata Fabrairu, ana sa ran gogayya ga raguwa na zabukan da ake shirin su gudana a kwanakin da ke tafe.

Abuja, Partei Kongress der in Nigeria regierenden APC
Hoto: DW/U.Musa

Bayan zaben na shugaban kasar da ke gudana yanzu, a ranar Lahadi ake sa ran zaben gwamnonin jam'iyyar da kuma ke zaman mafi zafi. An tsara zaben 'yan majalisar dattawa ranar 2 ga watan gobe na Oktoba a yayin kuma da ranar 3 ga watan za a gudanar da zaben majalisar wakilai ta kasar. Ranar 4 ga wata ne dai jam'iyyar ke fata na zabe na 'yan majalisar jihohi sannan kuma da gudanar da babban taro a ranar 6 ga watan da nufin tabbatar da takarar ta shugaban kasa.

Karikatur: Nigeria APC Streit
Hoto: DW / Abdulkareem Baba Aminu

To sai dai kuma APC ta saka kafa ta shure takarar biyu a cikin ministocin da suka hada Aisha Alhassan da ke da fata ta zama gwamna a Jihar Taraba da kuma Adebayo Shitu da ke zaman ministan sadarwa kuma mai neman ya zama gwamna a Jihar Oyo. Majiyoyi a fadar shugaban kasar dai sun ce tuni Aisha Alhassan da ta share shekaru uku da doriya tana ministan mata ta kasar ta rubuta takardar ajiye mukamin.