Najeriya za ta ba da hayar manyan filayen jiragenta | BATUTUWA | DW | 20.08.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Najeriya za ta ba da hayar manyan filayen jiragenta

A kokarin inganta sufurin jirgin sama a Najeriya, gwamnatin kasar ta ce za ta ba da hayar manyan filayen jiragen saman kasar guda Hudu. Sannan ta sayo karnuka na miliyan 600 domin aikin tsaro.

Nigeria Flughafen Lagos Archivbild 2007

Filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Lagos

A cikin wannan mako ne dai ma'aikatar sufurin saman Najeriya ta bude takardun bukatar ba da hayar manyan filayen jiragen saman kasar guda Hudu. Gwamnatin da ta kammala mai da tsohuwa yarinya a cikin filayen na Kano da Ikko da Fatakwal da ma babban birnin tarayya Abuja dai ta ce tana shirin ba da su ne haya ga ‘yan kasuwa.

Gwamnatin dai ta ce gazawar hukumomi na tafi da harkokin filayen da samun kudin shiga mai tsoka ne ya sanya ta tunanin komawa ga kasuwar da ke da alamar kwarewa a harkar. Hadi Sirika shi ne ministan sufurin na sama da ya ce tarrayar Najeriyar na bin sahu ne na manyan kasashen duniya da ke amfani da kasuwar domin inganta sufurin na sama.

Sama da Naira Miliyan dubu 30 ne dai ake jin an kai ga kashewa wajen sake fasalin kowane daga filayen da ke zaman babbar mashiga ta kasar daga sauran sassa na duniya. To sai dai kuma sabuwa ta dabarar da ta zo tun kafin ma sake kaddamar da sabobbin tashoshin dai na daukar hankalin kwarrarun da ke mata kallo na gazawa ga kokari na kare muradun kasar. Kaftin Bala Jibril dai kwarrare ne a harkar sufurin na sama da kuma ya ce hayar ta tashoshin ba za ta kai zuwa ga yin abin yabo a cikin masana'antar mai tasiri ba.

Koma ya take shirin kayawa a kokarin na tabbatar da zamani a cikin filayen na sama dai, tuni gwamnatin ta dora tare da sayen wasu karnuka na zamani domin aiki na tsaro. Karnunakan da za su lamushe Naira Miliyan 600 dai na shirin jawo kyashi daga ‘yan ina da kare da ma kaurayen da a idanunsu ba su da aikin da ya wuci farauta. 

To sai dai kuma a fadar Hadi Sirika karnukan na shirin maye gurbin na'u'rori na zamani wajen yakin kwaya da ma miyagu na makamai.

Abun jira a gani dai na zaman sabon yaki a tsakanin karnukan zamani da kuma dillalan kwayar da ke ta kara dabara  a Najeriyar a halin yanzu.

Sauti da bidiyo akan labarin