1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mun tanadi abincin da zai wadaci kowa a Najeriya

Ubale Musa AMA(ZMA)
August 4, 2022

A yayin da matsalar tsaro ke kara ta'azzara, gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce akwai tsimin abinci da zai wadatar da daukacin 'yan kasar da ke fuskantar barazana.

https://p.dw.com/p/4F8nD
Nigeria I Shugaba Buhari da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo (L)
Nigeria I Shugaba Buhari da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo (L)Hoto: Press Office Yemi Osinbajo

Daukacin sassan Najeriya daga arewaci zuwa tsakiyar kasar kusan duk cibiyoyin abincin tarrayar Najeriya na tafiya ne karkashin kulawar gaggan barayin dake cin karensu har gashi, lamarin da ke jawo gagarumin koma baya da damuwa cikin kasar da ma haifar da barazanar fuskantar matsalar wadata kasar da abinci.

Miliyoyin 'yan Najeriya na kallon tashin farashin abincin da aka dauki lokaci babu irinsa a matsayin wani sabon kangi da ma saka su a cikin kogin fatara da talauci, duk da yake mahukuntan Najeriya sun ce ba wata damuwa ta rashin isasshen abinci a kasar.

Karin Bayani:  Babu damuwa kan rashin abinci a Najeriya

Ministan noman kasar Mahmoud Mohammed yace "Akwai jerin matakai a bangaren gwamnatin tarayya da ke nufin tunkarar matsalar barazanar karancin abinci da ke neman bazuwa cikin kasar a halin yanzu."

Duk da wannan burin da gwamnatin Najeriya ta ke da shi batun rashin tsaron ya fara nuna alamun tasiri har ga yawan shinkafar da kasar ke takama da shan kwana akai na dada tasiri.

Nigeria I Dalar shinkafa don yaki da karancin abinci
Nigeria I Dalar shinkafa don yaki da karancin abinciHoto: Ubale Musa/DW

"Rashin Tsaro na shafar yankuna da dama da manoman shinkafa suke aiki" In ji Mohammed Sahabi Augie shugaban kungiyar manoman shinkafa a jihar Kebbi. Manoma da dama a jihohin Arewa maso yammacin Najeriya sun yi adabo da gonaki, inda suke tsoron komawar kilu zuwa babbar bau a yunkurin samun arziki daga noman.

Karin Bayani: Fargabar karancin cimaka bayan ta'azzarar matsalolin tsaro

Koma wane tasiri rashin tsaron ke iya yi bisa harkar noman, fadar mulki ta birnin tarayya Abuja ta ce shekaru Bakwai na gwamnatin kasar ya sauya da dama a cikin harkar noma a Najeriya, ko da yake idan har 'yan mulkin na buga kirjin nasarar sake dora kasar bisa taswirar noman, bisa dukkan alamu suna da sauran aikin burge 'yan kasar dake kallon tsadar kudin tuwo saboda tsadar kayan abinci da Najeriya ta fuskanta.