1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Najeriya ta lallasa Sudan a rukunin na hudu

January 15, 2022

Najeriya ta lallasa kasar Sudan da ci 3-1, a wasannin gasar kwallon Afirka da ci a halin yanzu a Kamaru. Najeriyar ta kara da Sudan din ne a birnin Garoua.

https://p.dw.com/p/45afK
Fußball | Africa Cup of Nations | Nigeria - Sudan
Hoto: Daniel Beloumou Olomo/AFP

Najeriya ta lallasa kasar Sudan da ci uku da daya, a wasannin rukuni na hudu da ake ciki a gasar kwallon Afirka mai ci a halin yanzu a Kamaru.

Dan wasan Najeriya Samuel Chukwueze ne ya fara zura kwallon farko a ragar Sudan wanda ya zaburar da Super Eagles din, sai kuma Taiwo Awoniyi ya zura ta biyu a ragar ta Sudan kafin zuwa hutun rabin lokaci.

'Yan dakikoki da komawa bayan hutun rabin lokaci, Moses Simon dan Najeriya, ya zura kwallo ta uku a ragar Sudan.

Sudan dai ta ci kwallon nata guda ne a bugun daga kai sai mai tsaron gida da Wlieldin Khedr ya ci mintuna 20 da komawa hutun rabin lokacin.

Yanzu dai Najeriya na da maki shida a wasanni biyu da ta buga ta kuma haye zuwa zagaye na gaba. A ranar Talata ne Najeriyar ta yi wa Masar daya mai ban haushi.