1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shin wutar lantarki ta inganta a Najeriya?

Uwais Abubakar Idris
April 11, 2024

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ta yi nisa da aiwatar da yarjejeniyar da ta kula da kasar Jamus a karkashin kamafanin Siemens inda ake sanya manya kuma ingantattun na'urorin da za su kyautata samar da wutar lantarki.

https://p.dw.com/p/4efY4
Manyan wayoyin lantarki a Najeriya
Manyan wayoyin lantarki a NajeriyaHoto: FLORIAN PLAUCHEUR/AFP via Getty Images

 

Sake zaburar da wannan yarjejeniya tsdakanin Najeriyar dea kasar Jamus a karkashin kamfanin Siemens bayan tsaiko da aka samu ne ya sanya samun uzuri na kamala shigo da daukacin naurorin da ake bukata na rarraba wutan lantarki da ma tashoshin tafi da gidanka a karkashin yarjejeniyar ta dalla milyan 2.3 a karkashin kasashen biyu. Domin tun baya ziyara da shugabanin kasashne Najeriya da Jamus suka kai kasashen juna ne aka ga wannan ci gaba. A yanzu gwamnatin Najeriya tace aiki ya yi nisa kuma an fara ganin tasirin hakan. Mr Adebayo Adelabu shi ne ministan kula da wutar lantarki na Najeriya wanda ya bayyana sun kusa kammala mataki na gwaji na wannan aiki domin duk kayan aikin suna Najeriya wadanda suka hada da manyan na'urorin rarraba wutar lantarkli guda 10 da tashoshin tafi da gidanka na wuta lantarki suma guda 10.

Karin Bayani: Karin farashin wutar lantarki na gigita 'yan Najeriya

Najeriya | wayoyin lantarki a Lagos
Wayoyin lantarki a NajeriyaHoto: Akintunde Akinleye/REUTERS

Gwamnatin dai ta bayyana cewa zata tabbatar da kamala aiwatar da wannan yarjejeniya da tun 2018 aka rattaba hannu a kanta a tsakanin Najeriya da kasar Jamus din musamman ganin fara tasirinta a yanzu. Ra'yoyi sun sha bamban a tsakanin masu amfani da wutan a fanin masu masana'antu. Alhaji Umar Zakari shine manajam daraktan kamfanin sarrafa leda da samar da talama a Najeriya ya tabbatar da cewa suna samun wutar. To sai dai ga Alhaji Yusuf Ladan shi ma mai kamfanin da ke amfanin da wutar lantarki ya ce su dai kam da sauran gyara.

Kwararru a fanin wutar lantarki dai sun dade da bayyana cewa baya ga matsalar samar da wutar lantarki a Najeriya, akwai ma kalubale na rarrabata domin kusan daukacin na'urorin sun lalace, abin da ya sanya Najeriyar sanya hannu a wannan yarjejeniya da gwamnatin kasar Jamus. Ma'aikatar kula da wutar lantarki ta Najeriya tana fusknatar kalubale na samarwa al'ummar kasar wutar lantarki ta kimanin sa'o'i 20 a kowace rana domin cika ka'ida game da ta karin kudi ga wadanda ke wannan rukuni, burin da yarjejeniyar tsakanin Jamus da Najeriya karkashin kamfanin Siemens ke taimaka kai wa ga cimma wannan buri.