Najeriya ta bude karin iyakokin ta da mokobta | Siyasa | DW | 15.01.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya ta bude karin iyakokin ta da mokobta

Gwamnatin tarayar Najeriya ta sanar da karin bude wasu iyakokin ta da sauran kasashe makobta wanda aka kwashe sama da shekara daya suna rufe. Hakan ya janyo martanin daga bangarori dabam-dabam a Nijar da Najeriya.

Tun bayan da gwamnatin Nijeriya ta sanar da bude sauran iyakokin kan tudun kasar al'umma ke cigaba da tofa albarkacin bakin su musamman wadanda ke kan iyakoki. Wakilin DW na Katsina ya ziyarci garin Jibiya da ke Iyaka da Jamhuriyar Nija domin jin yadda jama'a suka ji da sake bude iyakar. Da dama dai daga cikin wadanda DW ta yi hira da su, sun nuna murna da fainciki a game da sake bude iyakokin Najeriyar, wanda rufewar ta janyowa kasashen Nijar da Najeriya matsala ta ja da baya na al'amuran tattalin arziki a tsawon shekara daya. Gwamnatin Najeriyar dai a baya ta rufe Iyakar ta ne da sauran kasashe da nufin dakile shigowar haramtaccin kaya  irin sun shinkafa da makmai musamman yadda kasar ta shiga kalubalen tsaro. 

Sauti da bidiyo akan labarin