1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyya mai mulki a Najeriya na cikin rudani

June 17, 2020

A wani abun da ke zaman alamun shan kwaya a bangaren jam'iyyar APC mai mulki, akalla mutane uku ne dai ya zuwa yanzu ke ikirari na hallasci a shugabancin jam'iyyar, da tun da fari wata kotu ta dakatar a Abuja.

https://p.dw.com/p/3dvuv
Nigeria Oppositionspartei APC
Jam'iyyar APC mai alamar tsintsiya da ke mulki a Najeriya na shirin tarwatsewa.Hoto: DW/K. Gänsler

Guda daga cikinsu dai na ikirarin kotun ta Abuja ta tabbatar masa da shugabancin, yayin da guda kuma shugaban da kotun ta dakatar ya nada shi. Na ukun kuwa ya ce ya samo sabon hukunci daga wata kotun da nufin daukar ragamar masu tsintsiyar. Wannan idambarwa ta ikirarin shugabancin dai ta afku ne cikin sa'o'i 24 kacal, a wani abun da ke nuni da lalacewa a cikin lamuran jam'iyyar da ke tsaka a cikin rikici.

Tsintsiya na shirin watsewa?

Babu dai zato ba kuma tsammani, wata kotun daukaka kara ta dakatar da shugabancin Adams Oshiomhole a wani abun da ke kama da nisan rigima ta masu tsintsiyar.

Nigeria Wahlkampf von APC-Partei in Kano
Adams Oshiomhole na farko daga hagu yayin gangamin yakin neman zabe a KanoHoto: Salihi Tanko Yakasai

Tun kafin nan dai shi ma gwamnan jihar Edo da ake rikicin a kansa Godwin Nogheghase Obaseki dai ya ce ya bar APC bayan tsinewa shugabanci na Oshiomhole kafin sabo na hukuncin da ya yamutsa lamura kuma ke nuna irin jan aikin da ke gaban APC.

An dai kamalla wani taron majalisa ta gudanarwar jam'iyyar da kusan kaso biyu bisa ukunsu ke goyon bayan shugabancin Oshiomhole tare da yanke hukuncin tabbatar da Abiola Ajimobi da Oshiomhole ya nada a matsayin mataimakinsa daga sashe na Kudu, domin ci gaba a cikin harkokin APC kafin karshen kara ya zuwa kotun kolin da ya daukaka yau din nan.

Chief  Victor Giedom da ke zaman mataimakin sakataren jam'iyyar ta APC mai mulki a Najeriyar, kana  dan yankin na Oshiomhole ne dai tun da farkon fari ya nemi kotun ta dakatar da shugaban tare da ayyana masa jagorancin jam'iyyar. Bukatun kuma da ya yi nasara a cikinsu a matakan kotuna guda biyu bisa hujjar dakatar da Oshiomhole a matakin jam'iyyar na unguwarsa a Edo.

Lagos Taslim Balogun - Bola Tinubu
Tsohon gwamnan jihar Lagos Bola Ahmed TinubuHoto: Getty Images/AFP/P. Utomi

Kuma ya zuwa yanzu ana rabe a tsakanin 'yan goyon baya na Oshiomhole da ake ganin suna aiki tukuru da nufin kai wa ya zuwa bullar Bola Ahmed Tinubu a matsayin magaji na shugaban kasar a zabe na gaba, da kuma masu goyon bayan gwamnoni da ke neman kai karshen tabbatar da tasirin wasu gwamnonin masu sansana mulkin na Buhari

Taron gaggawa domin nemo mafita

Bala Jibril na zaman daya a cikin jigogin jam'iyyar da ke zargin kama karya a karkashin shugabancin na Oshiomhole kuma ya ce da abun da ke faruwa cikin APC. Ya kara da cewa ya zama wajibi 'yan kwamiti na gudanar jam'iyyar su kira babban taron kwamitin zartarwa da nufin kai wa ya zuwa taro na kasa domin warware takadamar mai zafi. A cikin tsakiyar kace nacen APC dai ana kallon gwagwarmaya ta mallakin ruhin jam'iyyar akan hanya ta takara ta shugaban kasa a zabe na gaba. Faruk BB Faruk dai na zaman wani mai sharhi a cikin harkoki na siyasar da kuma ya ce abun da ke faruwar yana shirin jefa masu tsintsiyar cikin tsaka mai wuya a hanyar mulkin. Shi kansa rikicin jihar ta Edo dai na nuna alamun jan aikin da ke cikin APC da ta rabe gida biyu a matakai daban-daban cikin kasar.