Wata kotu a Najeriya ta yi watsi da karan da jagoran 'yan Shi'a Ibrahim Zakzaky ya shigar a kan rundunar sojojin kasar wacce ya zarga da cin zarafin bil Adama.
Jagiran 'yan Shi'a Ibrahim Zakzaky ya nemi a biya shi diya ta Naira bliyan biyu bayan arangamar da aka sha tsakanin 'yan Shi'ar da sojojin Najeriyar. A cikin watan Disamba na shekara ta 2015 a garin Zariya da ke cikin jihar Kaduna a yanki arewa maso gabashin kasar wanda a ciki mutane 350 suka mutu.