Zariya na daga cikin manyan birane a jihar Kaduna kuma birnin da ke da dumbin tarihi idan ana magana kan jihar Kaduna a arewacin Najeriya.
A kan yi wa Zariya lakabi da birnin Ilimi saboda yawan cibiyoyin ilimin da birnin ke da shi domin a nan ne ake da jami'ar Ahmadu Bello wadda ta shahara a Najeriya da ma sauran sassan duniya.