Shi'a akida ce da wani bangare na musulmi a duniya ke bi. Iran da Iraki na daga cikin kasashen da ke da yawan mabiya tafarkin Shi'a.
A Najeriya ma da sauran kasashen Afirka ana samun 'yan Shi'a sosai. Galibin mabiya wannan tafarki ba sa shiri da 'yan Sunni saboda banbance-banbance da ke akwai tsakaninsu na akida.