Najeriya: Cutar Lasa ta bulla a Lagos | Labarai | DW | 09.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: Cutar Lasa ta bulla a Lagos

Hukumomin birnin Lagos a tarayyar Najeriya sun sanar cewa cutar zazzabin Lasa ta haddasa mutuwar mutane biyu, kuma an killace wasu mutane 100 don kauce wa yaduwar cutar.

Ärzte kämpfen weiter um das Leben des Lassa-Patienten (picture-alliance/dpa)

Lura da Masu cutar zazzabin Lassa

A cewar Farfesa Chris Bode, babban Daraktan asibitin koyarwa na jami'ar birnin Lagos inda aka kwantar da marasa lafiyar, cutar ta yi nisa a jikin mutanen biyu da aka kwantar kuma sun yi iyakar kokarin ceto su amma hakan bata samu ba. Daya daga cikin wadanda suka mutun wata mata ce mai shekaru 39 da haihuwa kuma ta na dauke juna biyu. Hukumar Lafiya ta duniya WHO ta bayyana cutar ta zazzabin Lasa a matsayin cutar da ke cikin dangin cutuka irin su Marburg da kuma Ebola, kuma cutar ta samu wannan suna ne daga wani yanki na arewacin Najeriya inda aka gano cutar a karon farko a shekara ta 1969. Birni na Lagos dai na da jama'ar da yawanta ya kai miliyan 20.