Mutuwar ′yan mata ta harzuka Najeriya | Labarai | DW | 08.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutuwar 'yan mata ta harzuka Najeriya

Gwamnatin Najeriya, ta bukaci cikakken binciken kasashen duniya dangane da mutuwar wasu 'yan kasarta, wadanda suka salwanta a kogin Bahar Rum.

Gwamnatin Najeriya, ta bukaci cikakken binciken kasashen duniya dangane da mutuwar wasu 'yan mata 26 'yan kasarta, wadanda suka salwanta a kogin Bahar Rum, a kokarinsu na shiga nahiyar Turai. A ranar Lahadin da ta gabata ne wani jirgin ruwan Spaniya, ya isa da gwarwakin 'yan matan a Italiya, inda aka ce aka yi bincike kan mutuwar tasu.

Ma'aikatar harkokin wajen Najeriyar da ke Abuja, ta ce ofishin jakadancin kasar na birnin Roma, ya ce wadanda suka mutun dai, mata ne da ke tsakanin shekaru 14 zuwa 18.

Masu bincike a Italiya, sun ce ga alamu 'yan matan an yiwo safararsu ne don zuwa harkar karuwanci a Turai, sai dai hukumar yaki da safarar bil adama ta Najeriyar, ta ce lallai ne sai an gudanar da cikakken binciken.